Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta shiryawa malaman makaranta karin moriya
2020-10-07 15:41:26        cri
Gwamnatin Najeriya ta alkawarta baiwa malaman makaranta sabon tsarin albashi, tare da tsawaita shekarun aikin su daga shekaru 35 zuwa 40, domin karfafa musu gwiwar ci gaba da ba da gudummawa.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ne ya bayyana hakan, cikin jawabin da ministan ilimin kasar Adamu Adamu ya karanta a madadin sa, albarkacin ranar malamai ta kasa da kasa.

Shugaba Buhari ya ce la'akari da muhimmiyar gudummawar da malamai ke bayarwa wajen ginin kasa, gwamnatin na fatan ingiza himmar su, ta yadda za su samu damar sauke nauyin dake wuyan su yadda ya kamata.

An dai tsara baiwa malaman firamare da na sakandare karin albashi na musamman, da guraben aikin yi kai tsaye, ga daliban da suka karanci fannin koyarwa daga jami'o'i da kwalejojin kasar. Kaza lika za a ginawa malamai dake aiki a yankunan karkara gidaje masu saukin kudi, da dai sauran tanade-tanade na gata ga malaman.

Da yake tsokaci game da hakan, babban sakataren kungiyar malaman makaranta ta NUT a kasar Mr. Mike Ene, ya shaidawa manema labarai a jihar Lagos cewa, daukacin malamai na matukar farin ciki da wannan sanarwa ta shugaban Najeriya, musamman duba da irin mawuyacin hali da suka tsuduma, tun bullar cutar COVID-19, wadda ta tilasa rufe makarantu dake dukkanin fadin kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China