Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta shiga atisayen sojojin ruwa a tekun Guinea
2020-10-08 15:25:46        cri
Rundunar sojin Najeriya ta shiga atisayen sojojin ruwa na kasashe 16, wanda ke gudana yanzu haka a tekun Guinea. A jiya Laraba ne dai rundunar sojojin ruwan Najeriyar ta aike da jiragen ruwan yaki 6, da kananan jiragen ruwa masu dauke da bindigogi 65 domin cimma nasarar atisayen.

Kwamandan dakarun Najeriyar Perry Onwuzulike ne ya jagoranci kaddamar da atisayen na yini 4. Mr. Onwuzulike, ya ce fatan su shi ne atisayen ya zamo hanyar bunkasa kwarewar sojojin ruwan a fannin gudanar da ayyukan tsaro tsakanin kasashen dake kewayen tekun Guinea.

Jami'in ya ce atisayen wanda ake gudanarwa duk shekara, gwamnatin kasar Faransa ce ke daukar nauyin sa, da hadin gwiwar Amurka da kungiyar tarayyar turai, da ma sauran abokan hulda.

Kasashen da suka shiga atisayen na bana dai sun hada da Amurka, da Faransa, da Italiya, da Brazil, da Angola, da Benin. Akwai kuma Kamaru, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. Sauran sun hada da Equatorial Guinea, da Gabon, da Ghana, da Ivory Coast, da Liberia, da Congo, da Sao Tome da Principe. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China