Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya: Fasahohin AI za su samar da damammakin cin gajiya daga fasahar sadarwa
2020-09-30 10:43:46        cri
Babban daraktan hukumar raya fasahohin sadarwa a Najeriya ko NITDA a takaice, Kashifu Abdullahi Inuwa, ya ce fasahohi masu nasaba da kwaikwayon tunanin bil Adama ko AI, suna kunshe da damammaki na bunkasa fasahar sadarwa a kasar, kuma za su taimakawa Najeriya wajen cimma muradun ci gaba mai dorewa na MDD ko SDGs nan da shekarar 2030.

Inuwa wanda ya bayyana hakan, yayin taron ranar kasa da kasa ta hakkin samun bayanai ga kowa, wanda ya gudana jiya Talata a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce fasahohin AI, na samar da damar kirkire kirkire, da damar inganta awon hadurra, da damar tsara komai yadda ya kamata, da yada bayanai cikin gaggawa.

Kaza lika babban jami'in na NITDA, ya ce fasahohin kwaikwayon tunanin bil Adama, da sauran fasahohi masu alaka, suna kyautata sauri, da ingancin tattara bayanai, a lokacin da ake bukasar musayar su, ko ake fatan sada duniya da su.

A farkon wannan wata ne dai gwamnatin Najeriya, ta ayyana shirinta na kafa cibiyar AI da mutum-mutumin inji, don cimma gajiyar tattalin arziki mai nasaba da wannan fanni na fasaha. (Saminu Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China