Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar
2020-10-05 15:40:19        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe 'yan bindiga da dama, gami da lalata maboyarsu masu tarin yawa, a wani hari ta sama da suka kaddamar kan kungiyar mayakan Boko Haram a jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafenta jiya Lahadi, mai magana da yawun hedkwatar tsaron Najeriya, John Enenche, ya bayyana cewa, wani bangare na dakarun rundanar Hail Storm-2, ya yi nasarar kashe mayakan Boko Haram da dama tare da lalata maboyarsu masu tarin yawa a yankunan Maima da Tusuy dake jihar ta Borno a ranar Alhamis da ta gabata, bayan samun rahotannin sirri da jerin leken asiri ta sama da suka gudanar, inda aka gano cewa, mayakan na haduwa a wuraren tare da kitsa kai hare-hare.

A cewarsa, dakarun mayakan sama, sun tura jiragen saman yaki da jirage masu saukar ungulu dake dauke da bindigogi, domin kai hari a wuraren biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China