Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude babbar muhawarar babban taron MDD karo na 75
2020-09-23 16:22:34        cri

Jiya Talata a birnin New York, hekwatar MDD, aka bude babbar muhawarar babban taron MDD karo na 75. Kimanin shugabanni ko kusoshi 170 daga kasashe daban-daban ne suka yi jawabai dangane da batun cutar COVID-19 da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da 2030, da matsalar sauyin yanayi, da sauran matsalolin kasa da kasa.

Shugaban babban taro na wannan karo Volkan Bozkır, shi ne ya jagorancin bikin bude taron. A jawabin da ya gabatar, ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya su tabbatar da kuma dukufa kan daidaita harkoki tsakanin bangarori daban-daban da amincewa da ci gaban da aka samu a wannan fanni a daidai wannan lokaci na cika shekaru 75 da kafuwar majalisar. Cutar COVID-19 ta kawowa bil Adama kalubale da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi, a don haka, dole ne kasashen duniya su yi watsi da bambancin ra'ayi da cika alkawarin da suka yi na gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban da hada kai don tinkarar wannan annoba tare.

A nasa jawabin, babban magatakardan majalisar Antonio Guterres ya bayyana cewa, kalubaloli dake addabar daukacin bil Adama a halin yanzu, su ne cutar COVID-19 da hadarin da ake ciki a shiyya-shiyya, da sauyin yanayi da kuma rashin amincewa tsakanin kasa da kasa, gami da halin maras kyau dangane da fasahar sadarwa. Ya kuma yi kira ga al'ummar duniya, da ta yi watsi da sabon nau'in yakin cacar baka da yaki da ra'ayi na kishin kai a fannin alluarar rigakafi tare kuma yin kira da a kawar da rashin daidaito ta hanyar kulla sabuwar yarjejeniyar al'umma da sabon tsarin tafiyar da harkokin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China