Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban taron MDD ya sanar da fara bikin cika shekaru 75 da kafuwar MDDr
2020-09-22 12:49:19        cri

A ranar 21 ga wata, MDD ta gabatar da taron koli na bikin tunawa da cika shekaru 75 da kafuwar MDDr, inda babban taron MDD ya amince da shirya bikin na cika shekaru 75 da kafa MDD, taron ya jaddada aniyar MDDr na tabbatar da samun dauwwamamman cigaba, da batun kare muhalli, da wanzar da zaman lafiya, da adalci, da samar da daidaiton jinsi.

MDDr ta yi alkawarin aiwatar da ajandar samar da dauwwamman cigaba nan da shekarar 2030 a bisa cikakken tsari kuma a kan lokaci, kana ta bukaci dukkan kasashen duniya su yi kokarin takaita fitar da sinadarai masu gurbata muhalli bisa dacewa da yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris. Taron MDDr ya jaddada cewa, halin da ake ciki a yanzu na rikice-rikicen kungiyoyin masu dauke da makamai, da barazanar zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, tilas ne a dauki matakan dakile su ta dukkan hanyoyi na lumana. Sanarwar ta yi alkawarin kiyaye dokokin kasa da kasa, da tabbatar da adalci, da kawar da duk wani tushen haifar da rashin daidaito. Yarjejeniyar ta yi alkawarin daga matsayin MDD ta hanyar yin sauye sauye, domin tabbatar da dorewar kudaden gudanarwar ayyukan MDDr, da kuma samun damar tinkarar kalubalolin da za a iya cin karo da su a nan gaba ta hanyar karfafa hadin gwiwar bangarori daban daban da nuna goyon baya ga juna.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China