Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana zaman rayuwa mai wadata a garin Yumai na yankin Tibet
2020-09-28 16:25:36        cri

Garin Yumai na gudunmar Longzi dake yankin Tibet mai cin gashin kansa, wanda ke kan iyakar kasar Sin, da ma mutane 3 ne kacal ke ci gaba da zaman rayuwa a wurin a karni da ya gabata, sakamakon tsananin wahalar rayuwa. Sai dai a shekarun baya-baya nan, garin ya canja fuska karkashin jagorancin gwamnatin kasar Sin da taimakon al'ummar kasar, yanzu ana zaman rayuwa cikin wadata a wannan wuri.

Ban da wannan kuma, an kara kyautata zaman rayuwar garin, a farkon rabin shekarar bana, an fara amfani da sabuwar hanya da ta hada garin Yumai da sauran wurare dake da tsawon kilomita 33, matakin da ya canja halin da garin ke ciki na wariya daga sauran wurare. Yanzu, mazauna garin suna zama cikin sabbin gidaje, kazalika suna da ganyen lambu dake dace da yanayi da ake ciki.

Shugaban gari Hu Xuemin ya nuna cewa, ya kamata a samar da muhalli masu kyau, da gabatar da matakai daban-daban, ta yadda za a kara kudin shigar jama'a, ta hakan al'ummar garin za su ci gaba da zama rayuwa mai nishadi a wannan wuri. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China