Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kawar da talauci ta hanyar ba da ilmi a lardin Anhui
2020-09-22 11:09:00        cri

Unguwar Maying ta gundumar Changfeng dake lardin Anhui, gari ne da aka mai da hankali matuka wajen gudanar da aikin kawar da talauci. An bullo da sabuwar hanyar dogaro da ba da ilmi da ba da tallafi da gudanar da aikin kirkire-kikire wato "Shirin Maying", ta yadda za a kawar da talauci bisa al'adu.

A shekarar 2014, an mai da wannan unguwar Maying wuri mafi muhimmanci da ake gudanar da aikin kawar da talauci, matasa sun fita waje don neman kudin shiga, inda suka bar yaransu a wurin, a don haka yana da wahala a ilmantar da wadannan yara. Saboda haka ne, darekta mai kula da harkokin kawar da kangin talauci na wannan wuri Zhong Yu a waccan lokaci yana ganin cewa, kamata ya yi a dora muhimmanci kan ba da ilmi ga yara don kawar da talauci. Wannan shiri ya hada da aikin kirkire-kirkire da ba da ilmi tare, matakin da ya kai ga kafa sana'o'i a wurin da tallafin dalibai ba tare da bata lokaci ba da yin tsimin kudade.

Masu ba da tallafi da kafa sana'o'i da dama sun yanke shawarar zama a Maying. Ya zuwa yanzu, an kafa kungiyoyin wasan kwaikwayo da hawan dokoki da fasahar sarrafa kayan tukwane da mutum-mutumin inji da dai sauransu 9, inda ake da malaman sa kai 256 da ma malamai 120.

Baya ga yadda yara a kauye suka bude idanunsu da kara ilmi ta wannan shiri, a bangare daya kuma, masu kafa sana'o'i sun cimma nasarar aikin kirkire-kirkire a wannan wuri. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China