2020-09-22 10:45:04 cri |
Gidauniyar bayar da agajin jin kai ta Red Cross ta kasar Sin, ta bayyana cewa, shirin agaji na baya-bayan da aka kaddamar, da nufin taimakawa manoman dake yankunan karkaka fita daga kangin talauci, zai kuma tallata kayan amfanin gona daga matalautan yankunan kasar kai tsaye.
Shirin mai suna "Charitable Kitchen" wanda ke fadakar da jama'a, zai sayar da kayan amfanin gona, ta hanyar tallata su kai tsaye ta kafar bidiyo.
Baya ga tallata kayayyakin amfanin gonar kai tsaye, za kuma a yi amfani da dandalin da mahalarta da dama suka shiga, a matsayin wani bangare na shirin kawar da talauci. Haka kuma shirin, kasancewarsa wani muhimmin mataki na farfado da yankunan karkara, zai mayar da hankali wajen hada kan rukunin jama'a wajen jagorantar aikin shirin kawar da talauci a yankunan karkara, da yayata sayar da kayayyaki masu inganci a sauran yankunan karkarar kasar, kamar yadda wani wani jami'in shirin Red Cross na kasar Sin ya bayyana.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China