Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mazauna kauyen Banyan sun kaura zuwa sabbin gidaje domin fita daga kangin talauci
2020-09-23 16:13:53        cri

Gunduma mai cin gashin kanta ta kabilar Tu na lardin Qinghai tana tsaunin Liupan, kuma wuri ne dake fama da talauci matuka. A watan Agusta na shekarar 2016, babban sakataren JKS Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a wurin, inda ya nanata cewa, kaura zuwa sabbin gidaje wata hanya ce mai kyau ta kawar da talauci. Hankalin kowa ya kwanta, wajibi a kiyaye matakan kawar da talauci, a kuma mai da hankali wajen kara karfin samar da kayayyaki. A shekarun baya-bayan nan, mazauna Banyan sun raya tattalin arziki ta hanyar dogaro da salon iri na kabilar Tu, matakin da ya fitar da su daga kangin talauci.

A shekarun baya, Lv Youjin yana zama a cikin tsauni mai tsayi mita 2700 kamar yadda kakakinsa suka yi. Kafin su kaura zuwa sabbin gidaje, akwai iyalai 129 dake fama da talauci saboda filaye marasa albarka da rashin kyan hanyoyi.

Sabo da haka ne, gwamnatin wurin ta yanke shawarar kaurar da su zuwa sabbin gidaje bisa nazarin da ta yi daga farkon shekarar 2016.

Bayan sun kaura zuwa sabbin gidaje dake gefen hanyoyin mota, ko wane iyali na da ruwa mai tsabta da wutar lantarki da kuma gas, Lv Youjin ya mallaki sabon gida mai fadin sama da muraba'in mita 200. Ban da wannan kuma, gwamnatin kauyen Banyan ta aiwatar da shirin kawar da talauci bisa halin da ko wane iyali ke ciki.

Kamfanin Panxiu wato fasahar saka mai fadin muraba'in mita 1500 da gwamnatin ta zuba kudi miliyan 3 wajen gina shi ya zama sha'ani mafi muhimmanci ga kauyen. Wannan fasahar saka ta kabilar Tu da ake kira "Panxiu" ta taimakawa mazauna wurin fita daga kangin talauci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China