Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in MDD ya yi alwashin kare tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban
2020-09-21 10:50:37        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, yayi amanna annobar COVID-19 ta sake bijiro da bukatar karfafa tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban a duniya, inda ya bayyana fatan cigaba da yin aiki tare da kasar Sin wajen tinkarar manyan kalubalolin dake addabar duniyar.

Jami'in na MDD yace, idan aka dubi yanayin da duniya take a halin yanzu, a bayyane take cewa duk wani kyakkyawan abu na gama gari ana iya samunsa ne ta hanyar kara yin hadin gwiwar kasa da kasa.

Babban sakataren ya kuma yi jawabi game da babbar gudunmawar da kasar Sin ke bayarwa wajen shawo kan kalubalolin duniya da kuma nasarorin da kasar ta samu a yaki da fatara.

Guterres ya bayyana kasar Sin a matsayin "Jigon hadin gwiwar bangarorin daban daban," jami'in MDD yace Sin tana ta kara taka muhimmiyar rawa a harkokin shiyya, da al'amurran kasa da kasa, ya kara da cewa, hadin gwiwar kut-da-kut da MDD ke yi da kasar Sin ya kara fadada zuwa bangarorin wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan duniya, wanda ya hada da nahiyar Asiya, Afrika, da yankin gabas ta tsakiya.(Ahamd)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China