Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in jin kai na MDD ya bukaci a gaggauta daukar matakan magance matsalar abinci
2020-09-18 10:50:03        cri

Babban jami'in kula da ayyukan jin kai na MDD Mark Lowcock, ya bukaci kasashe mambobin kwamitin sulhun MDD da su gaggauta daukar matakan magance matsalar abinci, kana su kara kyautata ayyukan jin kan bil Adama.

Ya fadawa taron kwamitin MDDr wanda aka gudanar game da yadda tashe tashen hankula suke haifar da yunwa cewa, annobar COVID-19 tana ci gaba da kara girman bukatar da ake da ita na kara fadada ayyukan jin kan bil Adama.

Jami'in yace, hukumomin bayar da agaji suna cikin tsaka mai wuya inda al'amurra ke neman gagararsu sakamakon karuwar bukatun da ake da su, kuma al'amurra za su kara tabarbarewa sakamakon rashin samun kudaden tallafin gudanarwa. Sai dai ya ce, akwai wasu muhimman matakai da ya kamata kwamitin sulhun da kasashe mambobin kwamitin sulhun MDDr su dauka domin tinkarar matsalar. Na farko, a yi kokarin yin kiraye kirayen neman zaman lafiya da tattaunawar siyasa domin kawo karshen tashen tashen hankula na kungiyoyin masu dauke da makamai. Na biyu, a tabbatar da kungiyoyin dake yaki da juna suna martaba dokokin hakkin dan Adam na kasa da kasa. Na uku, a yi kokarin rage mummunan tasirin matsin tattalin arziki da kungiyoyi masu dauke da makamai ke haifarwa da sauran tashe tashen hankula, sannan ya kamata a kara karfafa matakan samun kudade daga cibiyoyin samar da kudade na kasa da kasa.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China