Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Antonio Guterres ya yi kira da a yi hadin gwiwa don yakar COVID-19
2020-09-17 10:26:19        cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su yi aiki tare don yakar cutar COVID-19. Mr. Guterres ya ce wannan cuta ta zamewa duniya barazana mafi tsanani. Jami'in na wannan tsokaci ne a jiya Laraba, yayin wani taron manema labarai da ya gudana, inda ya ce cutar ta wajabtawa kasashen duniya bukatar yin hadin kai don yaki da tare.

Babban jami'in na MDD ya ce da yawa daga al'ummu na dora burin su kan alluran riga kafi, to sai dai kuma a gaskiya cutar COVID-19 ba ta da wani tartibin magani na kai tsaye. Kuma ita kanta allurar rigakafin da ake fatan samarwa, ba za ta warware matsaloli masu nasaba da cutar kwata kwata ba.

Daga nan sai jami'in ya bayyana cewa, dabara ita ce, fadada sabbi da tsoffin dabarun tunkarar wannan annoba, da kuma samar da jinya ga wadanda suka harbu da ita, don dakile ci gaban ta, da kare rayukan bil Adama, musamman cikin watanni 12 masu zuwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China