Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi Allah wadai da zargin da Amurka ta yiwa kasar ba gaira ba dalili
2020-09-12 20:51:08        cri
Jiya Juma'a, babban taron MDD ya zartas da kuduri mai alaka da yaki da cutar COVID-19, wakilin kasar Sin a jawabin da ya gabatar ya bayyana cewa, yayin da MDD take ingiza hadin kan kasa da kasa wajen yakar wannan mumunar cutar, Amurka ta sake maida fari baki inda ta dora laifi kan sauran kasashe, har ta yi yunkurin yada jita jita, Sin tana nuna rashin jin dadinta matuka.

Wakilin Sin ya ce, Sin ta shawo kan cutar cikin gajeren lokaci tare da baiwa sauran kasashen duniya taimako da tallafin kayayyaki ciki har da Amurka, duk nasarorin da Sin take samu ne a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminit ta kasar Sin da ma gwamnatin kasar bisa kokarin jama'ar kasar Sin baki daya, jama'ar ba zasu yarda duk wani ya jirkita gaskiya ko kuma bata sunan JKS ba.

Wakilin ya jaddada cewa, Sin ta yi kira ga kasashe mambobin majalisar dasu hada kansu don neman Amurka ta mutunta hakikanin halin da ake ciki na yakar cutar, da mutunta kimiyya da mai da hankali kan kiyaye rayuka da lafiyar jama'arta a maimakon yada jita jitar siyasa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China