Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude babban taron MDD karo na 75
2020-09-16 10:49:07        cri

Jiya Talata ne aka rufe babban taron MDD karo na 74, aka kuma bude taron karo na 75 a birnin New York hedkwatar majalisar.

An rufe taron na 74 ne da yamma, inda shugaban zaman majalisar na wannan karo daga tarayyar Najeriya Tijjani Muhammad-Bande, ya mika ragamar shugabancin majalissar, ga jami'in diplomasiyya dan kasar Turkiya Volkan Bozkir, daga baya kuma Volkan Bozkir ya buga gudumar dake alamta bude babban taro karo na 75. Babban magatakardan majalisar Antonio Guterres ya sheda sauyin shugabancin da ya guduna.

Bisa tanadin majalisar, za a rufe taro karon da ya gabata, kwana daya kafin bude sabon zama, sai dai kuma an yi sauyi ga ajandar taron a wannan karo, saboda yanayi na yaduwar cutar COVID-19.

A gun taron rufewar, Volkan Bozkir ya ba da jawabi, tare da yin rantsuwar kama aiki. A cewarsa, muhimman ayyuka a wa'adinsa, sun hadda da ingiza hadin kan kasa da kasa, da farfado da tsarin gudanar da ayyuka tsakanin bangarori daban-daban, da kare hakkin Bil Adama, da cimma muradun samun bunkasuwa mai dorewa kafin shekarar 2030, da ma samun daidaito, da adalci tsakanin jinsi daban daban da dai sauransu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China