Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron MDD ya amince da kudirin doka kan annobar COVID-19
2020-09-12 16:16:49        cri
Babban taron MDD da aka gudanar a ranar Juma'a ya amince da kunshin dokar karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a yaki da annobar COVID-19.

MDD ta nuna gamsuwa kan jagoranci da kuma rawar da hukumar lafiya ta duniya WHO ke takawa da kuma tsarin ayyukan MDD wajen tafiyar da ayyukan tinkarar yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a kasa da kasa, da kuma namijin kokarin da mambobin kasashen MDD ke yi a yaki da annobar.

Haka zalika, dokar ta nuna goyon baya kan kiraye kirayen babban sakataren MDD na neman a gaggauta tsagaita bude wuta a kasa da kasa, sakamakon fargabar da ake da ita game da tasirin annobar a kasashen dake fuskantar barazanar tashe tashen hankulla, tare da nuna goyon bayan cigaba da ayyukan wanzar da zaman lafiyar na MDD.

An bukaci kasashen mambobin MDD da dukkan masu ruwa da tsaki dasu karfafa shirin hadin gwiwar yaki da annobar COVID-19 da yin kandagarkin cutar, kana su fito fili su bayyana matsalar tare da daukar kwararan matakan kin jinin nuna wariya, nuna banbanci, da kalaman nuna kiyayya, da tashe tashen hankula da cin zarafi.

Sannan an bukaci kasashen dasu tabbatar an mutunta dukkan hakkokin bil adama, da kare 'yancinsu, da biyan muradunsu a yayin da ake kokarin kawar da annobar.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China