Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da dandalin nahiyar Afrika karo na 5 na bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na shekarar 2020
2020-09-07 19:52:42        cri
Yau Litinin, an gudanar da dandalin nahiyar Afrika karo na 5 na bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na shekarar 2020 a birnin Beijing.

Dandalin na wannan karo mai taken "Sabon zarafi ga Afrika bayan barkewar cutar COVID-19", ya nuna cewa Sin da Afrika na da makoma mai haske, ta fuskar hadin kansu a fannonin samar da manyan ababen more rayuwa, da ba da tallafin kudade, da ma bude kasuwanni tsakanninsu, karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya", da ma tsarin dandalin hadin kan Sin da Afrika, a lokacin da daukacin sassan duniya ke kokarin farfado da tattalin arzikinsu.

Babban sakataren dandalin ai gaban hadin kan kasashen Sin da afirka ta fuskar masana'antu Cheng Zhigang, ya yi jawabi da cewa, duba da ganin raguwar jari sosai, da kuma kayayyakin da kasashen yamma ke samarwa, da ma yadda cutar ke ci gaba da dabaibaye duniya, kara azama kan hadin kan kasashe masu tasowa zai taimaka, wajen kawar da illar da cutar ke haifarwa kasashen Afrika, da ma samar da sabbin kudade da nahiyar ke bukata a fannin raya masana'antu.

Dandalin nahiyar Afrika zai ingiza sha'anin masana'antun nahiyar, da ma karfafa gwiwar kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a Afrika, da kafa sassansu a nahiyar. A wani bangaren kuma, hakan zai taimaka wajen fitar da kayayyaki na musamman na nahiyar zuwa sauran sassan duniya, da ma kara hadin kan kamfanonin bangarorin biyu ta fuskar ciniki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China