Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Motocin da aka sayar a Sin a Yuli sun karu da 16.4% bisa makamancin lokacin bara
2020-08-11 15:46:32        cri
Kungiyar masana'antun motoci ta kasar Sin ta fidda rahoto a yau Talata cewa, a watan Yuli, adadin motocin da aka samar a kasar Sin ya kai dubu 2201, wanda ya ragu da 5.3%, idan aka kwatanta da na watan Yuni, kana, adadin ya karu da 21.9% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.

A sa'i daya kuma, an sayar da motoci da adadinsu ya kai dubu 2112, wanda ya ragu da 8.2%, idan aka kwatanta da na watan Yuni, kana, adadin ya karu da 16.4% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China