Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin da Amurka ba sa fafutukar neman iko
2020-08-31 11:10:34        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi jiya, a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Faransa, tare da amsa tambayoyin baki.

Shugaban cibiyar De Montbriar, ya yi tambaya cewa, Amurka ta ki amincewa da yuwuwar rasa matsayinta na babbar kasa a duniya, yayin da Sin da Faransa da Tarayyar Turai ke goyon bayan huldar kasa da kasa. Ta yaya ministan na Sin ke ganin za a kaucewa wani sabon yakin cacar baka tsakanin Sin da Amurka?

Da yake bada amsa, Wang Yi ya ce, babu bambancin a tsakanin dukkan kasashen duniya suke, kuma suna da hakkin neman ciyar da kansu gaba. Ya ce matsayar Sin ita ce, duniya na tunkarar wani yanayi na samun iko daga bangarori daban daban, kuma dole ne a inganta huldar kasa da kasa. Ya ce Sin ba ta muradin shiga yakin cacar baka da kowa. Ya ce kasashe sun hade kansu, tare da zama al'umma masu bukatu. A nan gaba, ya kamata a hada hannu wajen gina al'umma mai makoma ta bai daya kamar yadda shugaba Xi Jinping ke kira.

Bugu da kari, Wang Yi ya kara da cewa, akwai wasu batutuwa 3 da yake son bayyanawa dangane da dangantakar Sin da Amurka, na farko, bambancin ra'ayi ko sabanin dake tsakaninsu ba na neman iko ba ne. Na biyu, da alamu an bar Amurka da kakaba takunkumi ita kadai da kuma shafawa wasu bakin fenti. Na uku, kofar tattaunawa tsakanin Sin da Amurka, a bude take. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China