Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Farfadowar cutar COVID-19 yana da nasaba da taruwar mutane
2020-08-28 11:06:29        cri
Yayin taron manema labarai da aka yi a jiya Alhamis, babban dakataren hukumar kiwon lafiyar duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, kwanan baya, cutar numfashi ta COVID-19 ta dawo a wasu yankunan kasashen duniya, ya kamata kasa da kasa su dauki matakai wajen fuskantar wannan kalubale.

Ya jaddada cewa, idan akwai bukata, ya kamata a dakatar da aikace-aikacen taruwar mutane, ko kuma gudanar da irin wannan aiki ta hanyoyin da zasu dace, domin magance yaduwar annobar. Ya yi gargadi cewa, cikin watanni da dama masu zuwa, za a gudanar da bukukuwa iri daban daban a sassan kasa da kasa, dole ne a dauki matakai yadda ya kamata domin kare lafiya da tsaron mahalarta bukukuwa.

Haka kuma, cibiyar dakile yaduwar cutuka ta kasar Amurka ta fidda sabbin dabarun magance yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 a ranar 24 ga wata, inda ta bayyana cewa, idan akwai wani da ya taba haduwa da mai dauke da cutar COVID-19, in bai nuna alamun kamuwa da cutar ba, ba sai an yi masa gwajin cutar COVID-19 ba.

Dangane da wannan batu, darektar ba da jagorancin fasaha ta shirin gaggawar hukumar WHO Maria Van Kerkhove ta bayyana cewa, shawarar hukumar WHO ita ce, ya kamata a yi bincike kan duk wanda ke da nasaba da mai dauke da cutar, ko ya nuna alamun kamuwa da cutar, ko bai nuna ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China