Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai fama da cutar COVID-19 ta Amurka ta samu takardar kudin jinya da yawan gaske bayan an sallame ta daga asibiti
2020-08-23 16:59:29        cri

A halin yanzu, annobar cutar numfashi ta COVID-19 tana ci gaba da bazuwa cikin sauri a Amurka, don haka adadin rasa guraben aikin yi a kasar yana karuwa, a ranar 20 ga wata, ma'aikatar kula da 'yan kwadago ta kasar ta sanar cewa, a makon jiya adadin mutanen kasar wadanda suka gabatar da rokon neman samun kudin tallafi sakamakon rasa aikin yi a karon farko ya kai miliyan daya, abu mafi tsanani shi ne, Amurkawa wadanda suka rasa aikin ba su iya biyan kudin jinyar cutar, saboda ba su da inshorar lafiya bayan rasa ayyukansu.

Janet Mendez, wadda ta kamu da cutar, ta warke bayan jinyar da aka yi mata a asibiti har tsawon wata guda, kwanan baya ta zanta da 'dan jaridar gidan talibijin na Russia Today a birnin New York, inda ta bayyana cewa, kafin a sallame ta daga asibiti, sai dai iyalanta sun samu takardun neman kudin jinya da dama, kawo yanzu gaba daya adadin kudin jinyar ya riga ya kai kusan dala dubu 400, ban da inshorar lafiya, ita kanta za ta biya dala sama da dubu 75.

'Dan jaridar gidan talibijin na Russia Today ya tambaye ta, "Me ya sa kika samu takardun neman kudin jinya, saboda a baya gwamnatin Amurka ta taba sanar da cewa, za ta biya kudin jinyar COVID-19?"

Jenet Mendez ta ba da amsa cewa, "E haka ne, ni ma na yi mamaki, na ga labaran da aka bayar, inda gwamnatin kasarmu ta ce, kada a damu, idan an kamu da cutar COVID-19, za mu biya kudin jinya ga asibiti, amma yanzu dole ne ni kaina zan biya kudin jinya mai yawan gaske."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China