Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Birtaniya da Amurka na kokarin toshe hanyar samar da riga kafin COVID-19
2020-08-20 10:44:55        cri

Yanzu haka, daruruwan riga kafin COVID-19 a fadin duniya sun shiga matakan gwaji daban-daban, kuma ana sa ran samunsu nan ba da dadewa ba. Sai dai wasu manyan kasashe kamar Amurka da Birtaniya, sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da kamfanonin hada magunguna, domin tabbatar da an ba kasashensu fifiko wajen rabon riga kafin.

A ranar 14 ga wata, gwamnatin Birtaniya ta sanya hannu kan yarjejeniyar samar da riga kafin cutar da wasu kamfanonin Amurka biyu. Mujallar Ecologist ta Birtaniya, ta wallafa wata mukala a ranar 18 ga wata, inda ta ce, yarjejeniyar na barazana ga tabbatar da adalci wajen rabon riga kafin a duniya.

Mukalar ta bayyana cewa, Birtaniya na hada hannu da Amurka da kuma Tarayyar Turai, wajen gasar neman karin riga kafin a asirce. Kuma yarjejeniyar da suka rattabawa hannu, za ta rage adadin riga kafin na rukunoni masu rauni a matalautan kasashe, lamarin dake barazana ga kokarin yaki da annobar a duniya.

Kafar yada labarai ta Reuters ta ruwaito a ranar 18 ga wata cewa, darakta jnar na WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya aike da wasika ga dukkan mambobin hukumar, yana mai gayyatarsu da su shiga cikin shirin rabon riga kafin na duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China