Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban bankin duniya: Kila ne mutane miliyan 100 za su sake shiga kangin talauci sakamakon COVID-19
2020-08-23 16:32:05        cri

A kwanakin baya ne shugaban bankin duniya David Malpass ya yi gargadi cewa, mai yiwuwa ne al'ummun kasashen duniya kusan miliyan 100 za su sake shiga kangin talauci sakamakon tasirin annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Kafin wannan, bankin duniya mai hedkwatarsa a birnin Washington na Amurka ya yi hasashen cewa, mutanen da yawansu ya kai miliyan 60 za su yi fama da talauci mai tsanani sakamakon COVID-19, amma sabon hasashen ya nuna cewa, adadin mutanen da za su sake shiga kangin talaucin zai iya kaiwa miliyan 70 zuwa 100, shugaban bankin duniya Malpass yana mai cewa, idan ba a iya hana yaduwar annobar ba, kila ne adadin zai karu.

Kana bankin duniyar ya yi alkawari cewa, nan da watan Yunin shekarar 2021 mai zuwa, zai samar da tallafin kudin dala biliyan 160 ga kasashe 100 a fadin duniya, domin dakile al'amuran da za su faru cikin gaggawa, ya zuwa karshen watan Yunin bana, bankin ya riga ya samar da tallafin kudin da yawansa ya kai dala biliyan 21.

Amma abun bakin ciki shi ne, adadin mutanen da suke fama da talauci yana karuwa, shugaban bankin duniya Malpass ya bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin guraben aikin yi da aka samar yayin dakile annobar sun ragu, ban da haka, akwai wahala a samu abincin da ake bukata sakamakon tasirin cutar.

Malpass ya kara da cewa, idan ba a iya daidaita rikicin tattalin arziki a kan lokaci ba, mutanen da za su shiga kangin talauci za su karu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China