Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Kamfanin Lufthansa Ke Kallon Kasar Sin
2020-08-27 14:13:03        cri
A shekarar 2002, kamfanin Lufthansa dake Shenzhen wanda aka kafa bisa hadin kan kamfanin Lufthansa na kasar Jamus da kamfanin jiragen sama na Kailan na birnin Beijing, ya soma samar da hidimar gyara kayayyakin jiragen sama na kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na yankin Asiya da Pasific.

A yayin da waiwayi yadda kamfanin Lufthansa dake Shenzhen ke samun ci gaba bisa girman yankin tattalin arziki na musamman na Shenzhen a cikin shekaru kusan 20 da suka gabata, daraktan zartaswa na kamfanin Benjamin Scheidel dan asalin Jamus ya bayyana cewa, nasararin da birnin Shenzhen ya samu a cikin wadannan shekaru, sun jawo hankulan mutane sosai, kamfaninsa ya yi sa'ar gano ci gaban birnin da yankin musamman na Guangdong-Hong Kong-Macau.

Benjamin Scheidel ya kara bayyana cewa, a yayin da kamfaninsa ya soma gudanar da aiki, akwai jiragen saman daukar fasinja 250 ne kawai a kasar Sin, amma ya zuwa yanzu adadin ya karu zuwa kusan 4,000. Yanzu dai kasuwar jiragen sama na saurin bunkasuwa, kudin shiga da harkokin cinikayyar da kamfanin Lufthansa na Shenzhen ya samu ya karu.

A lokacin da annobar COVID-19 ta barke a bana, duk da tasirin da annobar ta yiwa sana'ar jiragen sama ta kasar Sin, amma bisa farfadowar tattalin arzikin kasar da karuwar yawan fasinjan dake shiga jiragen sama a kasar, harkokin cinikayyar kamfanin Lufthansa na Shenzhen ya farfado yadda ya kamata.

A matsayinsa na yankin musamman a fannin tattalin arziki a nan kasar Sin, birnin Shenzhen ya kasance birni mafi yawan matasa a cikin muhimman biranen dake yankin na Guangdong-Hong Kong-Macau, kana birnin da ya fi kyakkyawar makoma a nan gaba.

A cewar Benjamin Scheidel, "Ina fata birnin Shenzhen zai ci gaba da samun wadata da bunkasuwa, ina ma fatan ganin matakan yin kwaskwarima da kasar Sin ta kara dauka, za su gaggauta ci gaban birnin Shenzhen da ma yankin Guangdong-Hong Kong-Macau, ta yadda zai zama daya daga cikin yankunan bakin teku dake kan gaba a duniya. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China