Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shenzhen ya bayyana kuzarin tsarin bude kofa ga kasashen ketare
2020-08-19 14:09:43        cri


Jiya Talata, aka cika shekara daya da kafa yankin gwajin ba da misali ta fuskar tsarin mulkin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin a birnin Shenzhen. Yini daya kafin wannan rana, Shenzhen ya sanar da kafa tashoshi dubu 46 na fasahar 5G, matakin da ya sa wannan tsari ya shafi birnin baki daya, haka zalika ya zama wuri na farko a duniya da fasahar 5G ta mamaye.

Ban da wannan kuma, a wannan wata birnin zai cika shekaru 40 da kafuwarsa na yankin musamman na tattalin arziki. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, Shenzhen ya yi aikin gwajin tsarin kwskwarima a cikin gida da bude kofa ga waje don kokarin neman wata hanyar da ta dace, hakan ya sa Shenshen ya bunkasa zuwa wani birni mai kuzari dake tafiya da zamani, daga wata gunduma da ta yi fama da koma baya sosai. Har illa yau, Shenzhen na kokarin ba da gundumawa wajen raya tsarin mulkin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin.

An lura da cewa, a watan Oktoban shekarar 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanarwa duk duniya a Shenzhen cewa, Sin za ta nace ga hanyar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ba tare da tsayawa ba, haka kuma ya bayyana cewa, Sin za ta samu ci gaban da zai ba duniya mamaki a Shenzhen. A watan Agustan shekarar 2019, aka gabatar da shawarar majalisar gudanarwa ta kwamitin tsakiyar JKS game da kafa yankin gwajin tsarin mulkin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin. Ana iya ganin cewa, Shenzhen ya zama shaidar aiwatar da tsarin bude kofa a sabon matsayi.

A wannan karo kuwa, ba kawai abun misali Shenzhen zai zama ba, har ma da zama jagora. A farkon rabin shekarar bana, yawan GDPn yankin ya karu da kashi 0.1% bisa na makamancin lokacin a bara duk da ganin bullar cutar COVID-19, wanda ya zama birni mai girma na farko da ya samu irin wannan ci gaba a kasar Sin. Matakin da ya bayyana dalilin da ya sa Shenzhen ya zama abin koyi, kuma jagora ga tsarin kwaskwarima da bude kofa.

Kazalika, Shenzhen ya mai da aikin kirkire-kirkire a matsayin tsarinsa mai tushe, wanda ya samu babban ci gaba a wannan fanni dake jawo hankalin duniya baki daya, ba samar da wani dandanlin fahimtar ingantaciyyar bunkasuwar kasar Sin ga kasashen waje ya yi ba, har ma da nuna cewa, aikin kirkire-kirkire cikin 'yanci mataki ne mai tushe wajen ci gaba da aiwatar da tsarin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje. A sa'i daya kuma, Shenzhen ya zurfafa wannan tsari ta yadda zai zama a sahun gaba a fannin barin kasuwa ta yi halinta da aiwatar da harkoki bisa doka da ma kyautata halin ciniki tsakanin kasa da kasa da dai sauransu.

Abin da ya fi jawo hankalin mutane shi ne, Shenzhen ya cancanci sunan "abun misali" a kasar Sin tun daga lokacin kafa sansanin kare sirrin kasuwanci na farko a lardin Guangdong, zuwa ga kafa cibiyar ba da shawara ga rikice-rikice dangane da ikon mallakar fasahohi ta kasa da kasa, har ma zuwa ga zartas da gyararren shirin kare ikon mallakar fasahohi na yankin musamman ta fuskar tattalin arziki na Shenzhen.

Ban da wannan kuma, saboda ganin dama mai kyau na kafa yankin gulf na lardin Guangdong da Hongkong da Macao, Shenzhen ya gaggauta bude kofarsa ga kasashen waje. Bisa kididdigar da aka fitar, a farkon shekarar bana, Shenzhen ya kafa kamfanoni masu karbar jarin waje 2000, yawan kudin waje da ya yi amfani da shi ya kai dala fiye da biliyan 4, wanda ya karu da kashi 5% bisa na makamancin lokaci na bara.

Kokarin zama abun misali wajen aiwatar da tsarin mulkin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin, da kuma kokarin kara kuzarin bunkasa birni mai ba da misali kan aikin zamanintar da al'ummar kasar Sin hanya ce da Shenzhen ke bi. Karkashin wannan tsari, za a ga Shenzhen mai kuzari har ma da wata kasar Sin mai kuzari dake samar da damammaki mai kyau ga duk fadin duniya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China