Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shenzhen birni ne mai dumi
2020-08-26 18:54:03        cri

A yayin taron taya murnar cika shekaru 40 da fara aiwatar manufar yin gyare-gyare, da bude kofa ga ketare a nan kasar Sin, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya yi nuni da cewa, samarwa al'ummun Sinawa yanayin rayuwa mai dadi, tare kuma da farfado da al'ummun kasar Sin, babban aiki ne na 'yan JKS, kana buri ne na gwamnatin kasar, yayin da take aiwatar manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare.

Bisa matsayinsa na sabon birni mafi nuna kuzari a kasar Sin, har kullum birnin Shenzhen, wanda shi ne yankin musamman na tattalin arziki na farko na kasar, ya jawo hankalin masu kafa kamfanoni a fadin duniya.

Wasu alkaluma da aka fitar sun nuna cewa, a duk mutum 4 daya daga cikin mazauna birnin ya kafa kamfani.

Bugu da kari, sabon birnin yana matukar nuna kulawa ga matasan da suka shige shi domin cimma burinsu, duba da cewa gwammatin birnin, tana yin iya kokarin ta na samar da goyon baya gare su. Alal misali, gwamnatin birnin ta kafa hadadden dandalin samar da hidima ga matasa, wadanda suka zo Shenzhen don kafa kamfanoni, dandalin da ya kasance irinsa na farko a kasar Sin.

Baya ga kasancewar dandalin ya na samar da wurin kwana har tsawon kwanaki bakwai ga matasan da suka isa birnin a karo na farko, a daya hannun yana kuma ba su shawarwari yayin da suke neman samun aikin yi, inda kawo yanzu, irin wadannan dandalolin da aka kafa a birnin, suka riga suka kai 15.

A halin yanzu, adadin mutanen da suka kaura zuwa birnin Shenzhen ya dara na sauran biranen kasar Sin, saboda birnin ya kafa tsarin tabbatar da zamantakewar al'umma bisa matakai daban daban tun daga shekarar 2012, haka kuma ya fitar da manufofin ba da gata a jere ga ma'aikatan da suka isa birnin daga sauran sassan kasar. Misali, samar da hidimar kiwon lafiyar jama'a, da damar yin karatun ilmin tilas ga yaransu, da gidajen kwana ga wadanda suka dace da sharadin da aka tanada, har ma ana gaya musu cewa, "Idan har ka zo, to ka zama 'dan asalin birnin."

A watan Yulin bana, an shigar da birnin Shenzhen cikin birane goma mafiya dadin zaman rayuwa tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020. Ko shakka babu birnin Shenzhen ya cancanci yabon da aka yi masa. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China