2020-08-26 11:33:53 cri |
Yau, ranar 26 ga watan Agustan bana, yankin musamman na tattalin arziki na Shenzhen dake lardin Guangdong na kasar Sin ke cika shekaru 40 da kafuwa. A cikin wadannan shekaru 40 da suka gabta, birnin Shenzhen ya sauya daga wani karamin kauyen kamun kifi, zuwa babban birni na zamani, inda mazauna sama da miliyan 10 ke rayuwa, wanda hakan ya shaida manyan sauye-sauyen da aka samu a kasar Sin, tun bayan da aka fara aiwatar da manufar kwaskwarima.
A matsayinsa na yankin musamman na tattalin arziki na farko a kasar Sin, Shenzhen ya samu ci gaba cikin sauri a karkashin jagorancin shugabanni da dama.
"Jama'a: Barka da zuwa, babban sakatare
Xi: Barka dai, ko kuna jin dadin zama a Shenzhen?
Jama'a: Sosai!"
A ranar 8 ga watan Disamban shekarar 2012, babban sakataren JKS Xi Jinping, ya je dutsen Lotus dake cikin birnin Shenzhen, domin ajiye fure a gaban mutum-mutumin marigayi Deng Xiaoping. Daga baya ya dasa wani itacen banyan a wurin. Hakika a lambun shan iska na tsirrai na tafkin Xianhu na birnin Shenzhen dake kusa da dutsen Lotus, akwai wani itacen wani banyan, wanda marigayi Deng Xiaoping ya dasa a shekarar 1992, yayin da yake rangadin aiki a wurin, wanda ya bude wani sabon shafi na yin gyare-gayre da bude kofa a kasar Sin.
A yayin da ya gana da wasu tsoffafi wadanda suka rufawa marigayi Deng Xiaoping baya a lokacin da yake rangadin aiki a Shenzhen a shekarar 1992, Xi Jinping ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ya zabi birnin Shenzhen don zama wuri na farko da ya kai ziyara bayan ya zama babban sakataren JKS shi ne, yana son waiwayar tarihin dake bayyana yadda kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare cikin dimbin shekaru da suka gabata, ta yadda za a iya tabbatar da niyyar ci gaba da tafiyar da manufofin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare. Xi Jinping yana mai cewa, "Abubuwan da muka gani yanzu sun shaida cewa, manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare da kwamitin kolin jam'iyyarmu ta tsara, kuma ta aiwatar, ta yi daidai. Dole ne mu ci gaba da bin wannan manufar daidai da take kawo wa kasa da jama'armu karfi da kuma arziki."
Bayan da babban sakatare Xi ya tashi daga Shenzhen, ya sauka ne a biranen Zhuhai da Foshan da Guangzhou, inda ya sha jaddada cewa, yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, muhimmin mataki ne dake kawo kyakkyawan tasiri sosai ga makomar kasar Sin.
A watan Oktoban shekarar 2018, lokacin da aka cika shekaru 40 da fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare a kasar Sin, babban sakataren Xi ya sake zuwa Shenzhen, inda ya sake sanar da cewa, kasar Sin ba za ta daina yin kwaskwarima ba, haka kuma ba za ta daina bude kofa ga ketare ba.
"A cikin shekaru 40 da suka gabata, ci gaban da kasar Sin ta samu ya jawo hankulan kasashen duniya sosai. Wannan manufa ta kawo mana kyakkyawar makoma, dole ne mu ci gaba da aiwatar da ita nan gaba. Yanzu muna fuskantar wasu wahalhalu da matsaloli iri iri, dole ne mu warware da kuma shawo kan su ta hanyar neman ci gaban kasarmu."
Bisa jagorancin Xi Jinping, yanzu kasar Sin ta samu babban sakamako a fannoni daban daban. Alal misali an fara bunkasa babban yankin dake kunshe da wasu wuraren lardin Guangdong da yankin musamman na Hong Kong da na Macau, da gina yankin cinikiyya maras shinge na tsibirin Hainan. Sannan an aiwatar da manufar takaita sassan da baki 'yan kasuwa za su zuba jari, da kara habaka zumuncin dake tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa shawarar "ziri daya da hanya daya".
Abun farin ciki shi ne, duk da cewa ana yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 a yanzu, kasar Sin ba ta daina kokarinta na yin gyare-gyare ba, inda har ta dauki sabbin matakai a jere, domin kara kyautata ayyukan da take gudanarwa.
Kamar yadda shugaba Xi ya taba bayyanawa, idan ana son gina kasa ta zamani mai karfi dake bin salon gurguzu, to dole sai an ci gaba da yin kokari. (Jamila Zhou, Sanusi Chen)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China