Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Max Baucus: Ya kamata Sin da Amurka su yi shawarwari da hadin gwiwa
2020-08-22 15:59:04        cri
Kwanan baya, tsohon jakadan kasar Amurka dake kasar Sin Max S. Baucus ya bayyana cewa, ko da yake, dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka tana fuskantar matsala, amma ya kamata bangarorin biyu su yi shawarwari domin neman fannonin da zasu iya yin hadin gwiwa, da kokarin nuna girmamawa ga juna a yayin da suke fuskantar sabani a tsakaninsu.

A yayin da yake zantawa da dan jaridar People's Daily ta kasar Sin, Max S. Baucus ya ce, ministan harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya gabatar da wani jawabi, inda ya nuna shakku kan manufar da tsohon shugaban kasar Richard Nixon ya tsara dangane da harkokin Sin, kuma, ya ce, ya kamata a daina yin hadin gwiwa da kasar Sin. Amma, wannan mataki ba daidai ba ne, saboda zai kawo karin barazana da matsaloli.

Ya kara da cewa, ya kamata kasar Sin da kasar Amurka su yi shawarwari domin cimma matsayi daya kan wasu batutuwa, kamar yadda ya dace a fuskanci matsalolin sauyin yanayi, da ayyukan kiwon lafiyar jama'a, ciki har da tinkarar annobar cutar numfashi ta COVID-19, da kuma wasu batutuwan dake shafar nukiliyar kasashen Koriya ta Arewa da na Iran da dai sauransu. Kana, game da wasu batutuwa da kasashen biyu ba zasu iya cimma matsayi daya a kansu ba, ya kamata su nuna girmamawa ga juna, saboda, ba shakka, ko wace kasa zata dukufa domin kare moriyar kanta.

Haka kuma, Max S. Baucus ya jaddada cewa, ba za a raba dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka ba. A halin yanzu, wasu Amurkawa suna son kafa wata kungiyar hadin gwiwar kasa da kasa, da nufin kebantar da kasar Sin a duniya, wannan mataki bai dace ba, kuma ba za a iya cimma wannan buri ba. Sabo da a halin yanzu, ba wanda zai iya hana bunkasuwar kasar Sin. Shi ya sa, kamata ya yi kasar Amurka ta nemi wata hanyar yin hadin gwiwa da kasar Sin, ta yadda kasashen biyu za su iya cimma ra'ayi daya kan wasu batutuwa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China