Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karamin jakadan kasar Sin a Houston: za a daidaita yadda za a yi hadin gwiwa tsakanin Sin da kudancin kasar Amurka
2020-07-25 17:19:42        cri

Cai Wei, karamin jakadan kasar Sin da ke birnin Houston na Amurka, ya wallafa wata wasika a fili ga dukkan abokan kasar Sin dake kudancin Amurka, inda a cewarsa, gwamnatin Sin ba za ta dakatar da mu'amala tsakaninta da kudancin Amurka ba, kuma ba za ta dakatar da bauta wa Sinawa 'yan kaka gida ba. Ya ce ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka zai daidaita yadda za a yi hadin gwiwa tsakanin Sin da kudancin Amurka da sauran ayyuka.

A cikin wasikarsa, Cai Wei ya ce, a ranar 21 ga wata, Amurka ta tayar da fitina, inda ta bukaci Sin ta rufe karamin ofishin jakadancinta a Houston kwatsam, matakin da ya saba wa dokokin kasa da kasa da manyan ka'idojin raya hulda tsakanin kasa da kasa, da ma yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma kan kafa karamin ofishin jakadanci. Ya ce Amurka na yunkurin illata huldar da ke tsakaninta da Sin da gangan. Kasar Sin ta yi tir da hakan kuma tana adawa da shi. Cikin shekaru 41 da kulla huldar jakadanci tsakanin kasashen 2, hadin gwiwar dake tsakaninsu ta kawo musu alheri duka yayin da adawa da juna take illata moriyarsu duka. Ya ce ya kamata kasashen 2 su himmantu wajen mutunta juna, da hada kansu domin samun moriyar juna, a maimakon ta da rikici da nuna adawa da juna. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China