Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zargin da kasar Amurka ta yi kan karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Houston rade-radi ne
2020-07-27 20:24:32        cri
Game da zargin da wasu jami'an kasar Amurka suka yi a kwanan baya kan karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Houston, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau Litinin cewa, kalaman jami'an Amurka ba su da tushe, kuma rade-radi kawai.

A ranar 24 ga wata, a yayin da suke ganawa da manema labaru, manyan jami'an na ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka, da na ma'aikatar shari'a, da kuma hukumomin tattara bayanai na kasar sun ce, karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Houston ya dade yana satar asirin kasuwanci, da aikata ayyukan keta dokoki har ma da leken asiri.

Game da haka, Wang Wenbin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau cewa, karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake Hourton shi ne karamin ofishin jakadanci na farko da kasar Sin ta kafa a Amurka, bayan kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

A cikin shekaru 41 da suka gabata, ko da yaushe karamin ofishin yana kokarin inganta fahimtar juna a tsakanin bangarori daban daban na kasashen biyu, da kyakkyawan hadin kai a fannoni daban daban, kana da sa himma wajen ciyar da ayyukan sada zumunci a tsakanin kasashen biyu gaba, wanda hakan ya samu tabbaci sosai daga wajen al'ummar dake kudancin kasar ta Amurka.

Baya ga haka, Wang Wenbin ya nuna cewa, a cikin tsawon lokaci, wasu 'yan siyasa kalilan dake adawa da kasar Sin na Amurka, suna ta yada jita-jita don bata sunan kasar Sin, da nufin hana ci gaban kasar, da neman moriyar kansu. Kaza lika suna ta kara daukar matakai masu tsanani na tada fitina ga kasar Sin. Ainihin burinsu a bayyane yake, wato lalata dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, da kuma haifar da koma baya a tarihi. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China