Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akasarin ra'ayoyin jama'a na duniya sun goyi bayan matakin da kasar Sin ta dauka kan Amurka
2020-07-25 17:11:41        cri

Da safiyar jiya ne, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da ofishin jadakancin Amurka cewa, kasar Sin ta tsai da kudurin rufe karamin ofishin jakadancinta dake birnin Chengdu.

'Yan siyasa da masanan nazarin harkokin kasa da kasa na kasashen Palesdinu da Pakasitan da Rasha da Masar da Najeriya da Zambia da Iraki da kuma na Brazil suna ganin cewa, matakin da kasar Sin ta dauka ya yi daidai, ya dace da harkokin jakadanci. Kuma tsirarrun 'yan siaysan Amurka masu tunanin yakin cacar baki ne ya kamata su dauki alharin lamarin.

Ikenna Emewu, kwararren dan jarida a Nijeriya, kuma darektan zartaswa na cibiyar kafofin yada labaru na kasashen Afirka da Sin, ya yi bayani da cewa, kasar Sin ta dauki wannan mataki ne domin mayar da martani yadda ya kamata kan kudurin Amurka na rufe karamin ofishin jakadancinta dake Houston. Ya ce ba shakka Sin ta dauki matakin ne domin matakin da Amurka ta dauka. kuma Tsirarrun 'yan siyasan Amurka masu tunanin yakin cacar baki ne ya kamata su dauki alhakin lamarin. Ya kara da cewa, adawa da juna ba zai iya warware matsala ba, sai dai shawarwari. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China