Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin HK ta bayyana adawa da matakin Amurka na dakatar da wasu yarjejeniyoyi da suka cimma
2020-08-21 09:56:11        cri
Gwamnatin yankin musamman na HK ta bayyana adawa da kakkausar kalami, kan matakin gwamnatin Amurka na yin gaban kanta wajen dakatarwa ko katse wasu yarjejeniyoyi 3 da suka cimma.

Kakakin gwamnatin HK, ya ce gwamnatin yankin na adawa da matakin na Amurka, wanda take ganin wani yunkuri ne na haddasa rikici a dangantakar Sin da Amurka ta hanyar amfani da yankin.

A ranar Laraba ne ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da dakatarwa ko katse wasu yarjejeniyoyi 3 da gwamnatin HK da ta Amurkar suka cimma, wadanda suka hada da yarjejeniyar mika wadanda suka aikata laifuffuka da ta mika wadanda aka yankewa hukunci da kuma wadda ta shafi dauke haraji daga kudin shigar da aka samu na sufurin jiragen ruwa tsakanin kasa da kasa.

A cewar kakakin, yarjejeniyoyin ba na gatanci ba ne ga HK, domin an cimma su ne da zuciya daya, dake da nufin amfanawa al'ummomi da kasuwancin bangarorin biyu a fannonin doka da oda da sufurin jiragen ruwa da kuma batun haraji. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China