2020-06-30 20:26:12 cri |
A cikin sanarwar, jami'ar ta nuna cewa, kiyaye tsaron kasar nauyi ne dake wuyan yankin Hongkong, kuma gwamnatin yankin na maraba da wannan doka da kwamitin ya zartas a yau.
Ban da wannan kuma, ta ce gwamnatinta za ta kafa kwamitin kiyaye tsaron kasar, karkashin shugabancinta, bisa tanade-tanaden wannan doka ba tare da bata lokaci ba.
A hannu guda kuma, hukumar 'yan sanda, da sashin doka da shari'a, za su kafa hukuma ta musamman, don aiwatar da ayoyin dake kunshe cikin wannan doka. (Amina Xu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China