Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hong Kong: Yankin zai sauke nauyin dake wuyansa don kiyaye tsaron kasa bisa dokar dake da nasaba da hakan
2020-07-06 13:09:06        cri

Kantomar yankin Hong Kong Carrie Lam Cheng Yuet-ngor da sauran manyan jami'an gwamnatin yankin Hong Kong, sun bayyana a jiya Lahadi cewa, zartas da dokar tsaron kasar Sin dake da nasaba da yankin Hong Kong ya samu ci gaba mai armashi wajen tabbatar da manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu", kuma jami'an Hon Kong za su yi iyakacin kokari don aiwatar da ita, kuma sun yi imanin cewa, bayan jama'ar yankin sun fahimci dokar, za su bayyana kwarin gwiwarsu ga makomar yankin a nan gaba.

Kantomar ta ce, ana kokarin kiyaye tsarin mulki da tsaro da kuma cikakken yankin kasar don kare moriyar jama'a, tana mai cewa wannan doka ta shafi duk fadin kasar gaba daya.

Ban da wannan kuma, ta jaddada cewa, yankin zai yi namijin kokari don sauke nauyin dake wuyansa, da hada kai da masu ba da shawara kan tsaron kasar da hukumar tsaron kasar dake Hong Kong, ta yadda za a tsara da kyautata ayoyin doka da shari'a da kuma tsarin aiwatar da su yadda ya kamata don tabbatar da tsaro mai dorewa a yankin da kuma manufar "kasa daya mai tsarin mulki biyu" a cikin dogon lokaci. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China