Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da ofishin gwamnatin tsakiya na aikin tabbatar da dokar tsaron kasa a Hong Kong
2020-07-08 10:41:56        cri

Da safiyar Larabar nan ne aka kaddamar da ofishin gwamnatin tsakiya na kasar Sin, wanda zai rika gudanar da aikin tabbatar da dokar tsaron kasa a yankin Hong Kong.

Da yake tsokaci yayin kaddamar da ofishin, mataimakin darakta mai lura da harkokin Hong Kong da Macao na majalissar gudanarwar kasar Sin Luo Huining, ya ce sabon ofishin zai zamo wani ginshiki na tabbatar da tsaron kasa.

Luo ya kara da cewa, an dorawa ofishin alhakin tabbatar da aiwatar da dokar ta tsaron kasa, tare da sanya ido kan yadda ake aiki da ita bisa tanajin doka, ba tare da keta hakkoki, ko moriyar daidaiku, ko wasu kungiyoyi na al'ummar yankin ba.

An dai kafa wannan ofis ne bisa tanajin dokar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, wadda ta shafi tabbatar da tsaron kasa a yankin musamman na Hong Kong, dokar da kuma ta samu amincewa daga majalissar wakilan jama'ar Sin, aka kuma kaddamar da ita a Hong Kong a ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China