Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi ya tattauna da takwararsa ta kasar Kenya
2020-08-19 12:48:42        cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da takwararsa ta Kenya, Raychelle Omamo.

Yayin tattaunawar, Wang Yi ya bayyana godiya dangane da goyon bayan da Kenya ke ba Sin kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunta da wadanda ke ci mata tuwo a kwarya, ciki har da batun Taiwan da Hong Kong. Ya kara da cewa, Sin ma na goyon bayan Kenya ta taka rawa kan batutuwan da suka shafi yankin da take da kuma kasa da kasa, sannan a shirye Sin take ta karfafa hadin gwiwa da ita wajen daukaka manufofi da ka'idojin MDD da inganta huldar kasa da kasa da adawa da kariyar cinikayya da kuma kare muradun bai daya na kasashe masu tasowa tare da tabbatar da adalci a duniya.

A nata bangaren, Raychelle Omamo ta ce Kenya na godiya matuka ga taimakon da Sin ke ba ta wajen yaki da COVID-19 da kuma samun ci gaban kasa. Ta kara da cewa Kenya na goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, haka zalika tana goyon bayan kasar Sin wajen kare cikakken 'yancinta, kuma a shirye take ta hada hannu da ita wajen daukaka huldar kasa da kasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China