Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi jigilar furanni daga kasar Kenya zuwa kasar Sin ta jiragen sama
2020-02-28 15:32:11        cri
Rahotanni daga kasar Kenya na cewa, kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na China Southern na kasar Sin, ya dawo da harkokinsa na zirga-zirga zuwa Nairabo, babban birnin kasar ta Kenya, bayan dakatar wa na makonni biyu, sakamakon annobar COVID-19 da ta bulla a kasar Sin. A ranar Laraba da dare ne kuma aka yi lodin sama da tan daya na furanni daga kasar ta Kenya zuwa kasar Sin kai tsaye ta jiragen saman.

Jami'in kamfanin jiragen sama na China Southern dake Nairobi, He Qinwen, wanda ya yi shigo da furannin na Kenya zuwa kasar Sin a jiya Alhamis shi ne ya sanar da hakan, yana mai cewa wadannan furannin da ake nomawa a tsaunuka masu inganci sun fito ne daga gonakin yankin guda 10.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China