Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi taron farko na tattauna hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Kenya
2019-05-29 11:07:58        cri

An yi taro karo na farko na tattauna hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Sin da Kenya a fannin cinikayya da zuba jari, da kimiyyar tattalin arziki a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, wanda mataimakin ministan ciniki na kasar Sin Mista Qian Keming, da mataimakin ministan masana'antu, ciniki da hadin kai na Kenya Mista Chris Kiptoo suka jagoranta.

Wannan shi ne taro karo na farko, tun bayan daga matsayinsa daga kwamitin ciniki zuwa kwamitin tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen biyu, da zummar tabbatar da matsayar da shugaba Xi Jinping da Uhuru Kenyatta suka cimma cikin ganawar da suka yi har sau uku cikin gajeren lokaci, da kuma matakai 8 da za a dauka a wannan fanni, wadanda aka cimma matsaya kansu, yayin taron koli na dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika, ta yadda kasashen biyu za su hada gwiwar tattalin arziki da cinikayya a wasu lokuta masu zuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China