Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar WBAK za ta yi amfani da fasahohin kasar Sin wajen kara samar da tsaftataccen ruwan sha
2019-11-08 09:26:45        cri
Shugaban kungiyar kamfanonin samar da ruwan kwalba na kasar Kenya (WBAK) Henry Kabogo, ya bayyana cewa, kungiyar na shirin kara amfani da fasahohin kasar Sin, don inganta samar da ruwa mai tsafta a kasar.

Heny Kabogo, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobin Kenya cewa, batun samun ruwan sha mai tsafta, na daga cikin kalubalen da birane da yankunan karkarar kasar ke fuskanta.

Jami'in ya bayyana haka ne, yayin babban taron shekara-shekara na kungiyar, yana mai cewa, kamfanonin samar da ruwan kwalba, sun fi son amfani da fasahohin kasar Sin a kananan kamfanonin dake samar da ruwan kwalba mai tsafa , don magance matsalar ruwa da al'ummomin yankunan kasar ke fama da ita.

Kabogo ya kara da cewa, kafin fasahohin samar da ruwan kwalba na kasar Sin su shigo cikin kasar, al'ummomi masu matsaikaci da manyan kudin shiga ne ke iya sayan ruwan da aka sarrafa.

Shugaban ya lura da cewa, fasahohin na kasar Sin, sun kuma canja tsarin samar da ruwan sha mai tsafta, inda a kalla kanana da matsakaitan kamfanoni 700 ke rike da kimanin kaso 70 cikin 100 na jarin kasuwar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China