Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gazawar Amurka na sabunta matakan rage radadin COVID-19 zai yiwa tattalin arzikin barazana
2020-08-14 11:25:47        cri
Wani sabon rahoto da aka fitar, ya nuna cewa, rashin fahimta da aka fuskanta a majalisar dokokin kasar Amurka game da sake sabunta wa'adin shirye-shiryen magance tasirin da cutar COVID-19 ta yiwa tattalin arzikin kasar, tana yiwa tasirin shirye-shiryen barazana da kara yiwa tattalin arzikin kasar illa, saboda matakan kulle da ake aiwatarwa a kasar.

Babban jami'i a jami'ar nazarin tattalin arziki ta kasa da kasa ta Peterson(PIIE) Sherman Robinson da Raul Hinojosa-Ojeda, babban darektan cibiyar bunkasuwa da hadin gwiwa ta UCLA, su ne suka rubuta sharhin da aka wallafa ranar Laraba. Masanan biyu sun bayyana cewa, idan aka rage tallafin da ake baiwa iyalai zuwa dala biliyan 500, to, akwai hasashe dake nuna cewa, tasirin ka iya jefa kasar ta Amurka cikin matsalar tattalin arziki, inda kasar za ta yi hasarar da ta kai kaso 3.8 zuwa kaso 5 cikin 100 na GDPn ta da karuwar kaso 4 zuwa 5 cikin 100 na marasa aikin yi .

A don haka, sun bukaci masu tsara manufofi na kasar, da su ci gaba da aiwatar da tsarin tallafin da ake bayarwa, don rage matsin lambar tattalin arzikin da tuni ya gamu da illa. Suna masu cewa, tsarin da mahunkuntan Amurkar ke son aiwatarwa a halin yanzu, ba zai yiwa yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu kyau ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China