Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin kula da cinikayyar Amurka da Sin: Ana fatan alheri kan ci gaban huldar da ke tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da ciniki
2020-08-12 16:00:00        cri

A ranar 11 ga wata, kwamitin kula da cinikayyar kasashen Amurka da Sin ya kaddamar da rahoton shekara-shekara dangane da yanayin kasuwancin kasar Sin, inda ya ce, ko da yake kasashen 2 sun gamu da matsala wajen raya huldar da ke tsakaninsu yayin da annobar cutar COVID-19 ke yaduwa a duniya, amma kamfanonin Amurka da ke kasar Sin ba su bar kasar Sin ba, kana sun nuna imani kan makomar kasar Sin ta fuskar kasuwanci a shekaru 5 masu zuwa. Ana kuma fatan alheri kan ci gaban huldar da ke tsakanin Amurka da Sin ta fuskar tattalin arziki da ciniki, duk da yaduwar annobar ta COVID-19 da kuma dalilai na siyasa.

A cikin rahoton, kamfanonin Amurka da aka tambaya suna ganin cewa, huldar da ke tsakanin Amurka da Sin da kuma illar yaduwar annobar suna daga cikin manyan kalubaloli guda 10 da za su fuskanta a shekarar 2020. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China