Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana da imanin cewa kasashen duniya ba za su yarda Amurka ta yi babakare kan fasahar 5G ba
2020-08-14 20:32:13        cri

Yau Juma'a, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa manema labarai cewa, Amurka ta siyasantar da batun fasahar 5G, ta kuma kafa wasu kungiyoyin kawancen ta, tare da kebe su, matakin da zai hana bunkasuwar fasahar 5G, ya kuma sabawa ka'idar yin takara bisa adalci, da ma keta muradun kasashen duniya baki daya.

To sai dai kuma a cewar Zhao, Sin na da imanin cewa, kasashen duniya suna da masaniyar hakikanin manufar wasu 'yan siyasar Amurka, kuma ba za su amince da duk wani babakare da Amurka ke yi a fannin hadin kai da sauran kasashe dangane da fasahar ta 5G. Kasashen duniya za su yi kokari tare wajen kiyaye yanayin kasuwanci bisa adalci da daidaito, da bude kofa, da ma kawar da banbancin ra'ayi.

Rahotanni sun nuna cewa, yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ziyarci kasar Slovenia, ya kulla wata hadaddiyar sanarwa da takwaransa na kasar, don gane da tsaron Intanet dake da alaka da fasahar 5G. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China