Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka Ta Sa Kawayenta Neman Nisanta Kansu Da Ita
2020-08-12 20:32:43        cri

Bayan da kasar Amurka ta sanar da janye jikinta daga hukumar lafiyar duniya ta WHO, kasar ta ci gaba da neman jagorantar wani aikin gyaran fuska a cikin hukumar, lamarin da ya fusata kasashen da suka hada da Jamus da Faransa, ta yadda kasashen 2 suka janye jiki daga wata muhawarar da ake yi bisa inuwar kungiyar G7 mai nasaba da batun. Wannan dai alama ce dake nuni ga yadda ake samun matsalar dangantaka tsakanin Amurka da manyan kawayenta.

Rahotannin sun ce, karkashin jagorancin kasar Amurka, kasashen kungiyar G7 sun riga sun kwashe wasu watanni 4, suna tattauna batun gyare-gyare kan hukumar WHO har sau 20. Amma zuwa yanzu, kasashen Jamus da Faransa sun janye jiki daga muhawarar. Ta hakan za a iya ganin cewa, kasar Amurka ta cika son kanta, yayin da take neman gyaran fuska ga WHO, lamarin da ya fusata kawayenta sosai.

Hakika wasu kasashen Turai sun dade ba sa jin dadin wasu manufofin kasar Amurka. Bayan barkewar annobar COVID-19 a duniya, wasu 'yan siyasar kasar Amurka sun yi biris da gargadin da kasar Sin, da hukumar WHO suka yi mata, lamarin da ya sanya cutar samun bazuwa cikin matukar sauki a kasar. Duk da haka, kasar Amurka na neman siyasantar da batun, da dora laifi ga sauran kasashe. Batun ya janyo suka daga gamayyar kasa da kasa, cikin har da wasu tsoffin abokananta.

Haka zalika, yadda ake samun sabanin ra'ayi tsakanin kasashen yamma a wannan karo, ya shaida wani yanayin da ake ciki, na samun rarrabuwar kawuna tsakanin wadannan kasashe. A ganin kasashen Turai, ba za a samu dakile wani babban kalubale, kamar cutar COVID-19 ba, har sai an tsaya kan ra'ayin cudanyar bangarori daban daban masu fada a ji a duniyarmu.

Idan mun maimaita baya, za mu ga yadda wasu 'yan siyasar kasar Amurka ke kokarin neman ta da zaune-tsaye a duniyarmu, lamarin da ya fusata abokanta na kasashen Turai matuka. Sau da yawa, kasar Amurka ta keta ka'idojin kasa da kasa, da lalata moriyar bai daya ta gamayyar kasa da kasa, inda sannu a hankali, take neman mai da kanta saniyar ware. Idan kasar ba ta daidaita manufarta ba, to, tabbas ne, karin kasashe za su nisanta kansu da ita a nan gaba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China