Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka na da jan aiki a gabanta
2020-08-12 16:58:18        cri

Yayin da wasu kasashe kamar kasar Sin suka ga bayan cutar numfashi ta COVID-19, har ma masana'antu da ma'aikatu da sauran hidimomi suka farfado yadda ya kamata, amma har yanzu Amurka na fama da wannan annoba, inda cibiyar nazarin tsare-tsaren kimiyya da aikin injiniya ta jami'ar Johns Hopkins (CSSE) ta bayyana cewa, adadin wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Amurka, ya zarce miliyan biyar,

Kana yawan wadanda cutar ta hallaka ya kai 162,441. Abin da malam Bahaushe ke cewa, wankin Hula yana kokarin kai Amurka dare.

Wani hasashe da cibiyar kula da harkokin kiwon lafiya da kididdiga (IHME) a jami'ar Washington ta yi na nuna cewa, nan da ranar 1 ga watan Disamba dake tafe, cutar za ta hallaka mutane da yawansu ya kai dubu 300 a kasar ta Amurka.

Sai dai maimakon mahukuntan Amurkar su mayar da hankali wajen kare rayuka da lafiyar Amurkawa, wasu 'yan siyasar kasar sun karkata wajen dakushe kamfanoni da tsamo baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da neman shafa mata bakin fenti. Wato sun bar Jaki suna bugun teki.

Amurka dai tana fakewa da batun tsaro wajen daukar matakan da ba su dace ba kan kamfanonin kasar Sin, musamman na baya-bayan nan kan manhajar Tik Tok, saboda yadda manhajar ta fi wasu kamfanonin Amurka karbuwa.

Amma duk da wani sabon salon yakin cacar baka da Amurka ta bullo da shi, hakan bai hana manyan kamfanonin kasar zuba jari a cikin kasar Sin ba. Wannan shi ne wayon a ci an kori Kare daga gindin Dinya.

Koma dai mene ne, kamata ya yi kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya su warware duk wani sabani da ma bambance-bambancen dake tsakaninsu cikin lumana da fahimta da mutunta juna, duba da yadda kowa ne bangare ke amfana da juna.

Labari mai dadi game da batun samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 da darektan cibiyar cututtuka masu yaduwa ta Amurka, kana mamba a kwamitin yaki da cutar COVID-19 ta fadar White House Dr. Antthony Fauci, ya bayyana cewa, sakamakon gwajin allura da aka yi kan dabbobi da bil-Adama, sun nuna cewa, akwai tabbacin za a samar da riga kafin da ba shi da wani hadari kuma mai inganci, nan da karshen wannan shekara ko farkon shekara mai zuwa, bai kamata Amurka ta mike kafa tana jiran tsammanin marabbuka ba, wai malam ya ki noma don zakka. Ya kamata ta mayar da hankali wajen ceto rayukan daruruwan 'yan kasar dake salwanta a kowace rana, sakamakon Covid-19, maimakon siyasantar da batun da ma kokarin neman kuri'a da madufun iko fiye da jama'arsu ba, tun da sai da mutane za a yi batun shugabanci. Wai mutane su ne kasuwa ba tarin rumfuna ba. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China