Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan 'yan siyasar Amurka na keta yarjejeniyar da ta shafi batun Taiwan
2020-08-10 21:05:29        cri

A jiya Lahadi, minista mai kula da lafiya da batun samar da hidimomi ga jama'a na kasar Amurka, Alex Azar, ya isa yankin Taiwan na kasar Sin, sa'an nan a yau Litinin ya gana da madugan yankin, lamarin da ya keta yarjejeniyar da kasashen Sin da Amurka suka kulla a baya, game da manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. Saboda haka gwamnatin kasar Sin ta riga ta nuna takaicinta ga bangaren Amurka. Kuma ya kamata wasu 'yan siyasar kasar Amurka su sa lura, don kar su ci gaba da samar da wata alamar kuskure ga wasu mutanen dake neman balle yankin Taiwan daga kasar Sin, matakin da tabbas zai haifar da babbar matsala gare su.

Sanin kowa ne, manufar kasar Sin daya tilo a duniya, tushe ne ga huldar dake tsakanin kasar Amurka da kasar Sin. Bisa wata yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen 2, ya kamata kasar Amurka ta kalli gwamnatin jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, a matsayin hukumar halas daya tak ta kasar. Sa'an nan bai kamata ba, Amurka ta yi musaya da Taiwan bisa matsayi na hukuma.

A wannan karo, minista Azar na kasar Amurka, ya yi amfani da wani dalili, wai yana neman kulla huldar hadin kai tare da Taiwan don tinkarar cutar COVID-19, don samun damar ziyartar yankin. Sai dai a wannan lokaci da ake fama da annoba a yankin Taiwan, hukumar yankin ta cire dokar killace kai a cikin wani daki har wasu kwanaki 14, domin Alex Azar da 'yan tawagarsa, lamarin da ya yi matukar fusata jama'ar yankin Taiwan.

Hakika masu nazarin al'amuran duniya sun san dalilin da ya sa mista Azar zuwa yankin Taiwan, wato dai neman biyan bukatu a fannin siyasa, inda zai nemi kyautata huldar dake tsakanin kasar Amurka da yankin na Taiwan, da kara janyo hankalin jama'ar kasar Amurka zuwa ga wani batun da ya shafi kasar Sin, maimakon sanya su lura da matsaloli masu dimbin yawa da ake fama da su a cikin gidan kasar Amurka.

Idan mun dubi wasu matakan da kasar Amurka ta dauka dangane da yankin Taiwan, inda ta kara kokarin sayar da makamai ga yankin, da tura wani babban jami'i don ziyartar yankin, za mu san cewa, wadannan matakai ne masu hadari, dake iya tsananta yanayin da ake ciki a mashigin tekun na Taiwan.

Da ma dai batun Taiwan ya shafi babbar moriyar kasar Sin, wanda kuma ya kasance batu mafi muhimmanci da ke yin tasiri ga huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Saboda haka, yadda 'yan siyasar kasar Amurka suka dauki wannan matakin da ya shafi Taiwan, zai haddasa karin rashin tabbas ga huldar bangarorin 2. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China