Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takunkumin da Sin ta kakabawa wasu Amurkawa ya dace da martani
2020-08-11 20:39:48        cri

Jiya Litinin, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da kakkabawa wasu Amurkawa su 11 takunkumi, bisa ayyuka marasa kyau da suka aikata game da batun yankin Hongkong. Wannan mataki ya zama martani da kasar Sin ta mayarwa Amurka, bayan da Amurkan ta sanyawa wasu jami'an gwamnatin tsakiyar kasar Sin da ma wasu dake yankin HK makamancin wannan takunkumi.

Daga cikin jerin sunayen da kasar Sin ta ambata, cikin jami'an Amurka da aka kakabawa takunkumin akwai 'yan majalisun kafa dokokin Amurka, da ma shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda suka dade suna tsoma baki cikin harkokin HK, har ma suka jirkita gaskiyar tsarin "kasa daya kasancewar tsarin mulki iri biyu", da kuma rurar wutar tawaye, da zummar ta da zaune tsaye a HK.

Matakin da Sin ta dauka a wannan karo ya nuna cewa, Sin za ta tsaya tsayin daka wajen yin iyakacin kokarin kiyaye ikon mulki da tsaro, da muradunta dake da nasaba da bunkasuwar kasar ba tare da ja da baya ko kadan ba.

Ban da wannan kuma, wannan mataki mai dacewa, ya zama wajabi wajen mayar da martani ga Amurka, da ma kiyaye dangantakar kasa da kasa bisa tsarin demokuradiyya. Tsaida dokar tsaron kasa, ikon kowace kasa ne. Shisshige da Amurka ta yi kan aikin tsayar da dokar kasar Sin, ya keta ka'idar dangantakar kasa da kasa. Martani da Sin ta yiwa Amurka ya kiyaye ikon mulki da kimar kasar, kuma ya bayyana matsayin da Sin take dauka na nacewa ga ka'idar dangantakar kasa da kasa.

Shin ko wasu 'yan siyasar Amurka ba su san halin da suke ciki ba, duk da cewa dokar tsaron kasar dake da alaka da yankin HK na samun karbuwa matuka daga jama'ar HK? Yaki da kasar Sin ba zai kawo musu moriya a siyasance ba ko kadan. Matakin da suka dauka na sabawa zukatan jama'a, da ma halin da duniya ke ciki. Idan ba su dakatar da irin wannan wasa ba, za su ci tura daga tushe. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China