Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da COVID-19 ta kashe a Afrika ta kudu ya zarce 10,000
2020-08-09 16:43:38        cri
Ministan lafiyar kasar Afrika ta kudu Zweli Mkhize, ya sanar a ranar Asabar cewa, mutanen da cutar COVID-19 ta hallaka a kasar ya zarce 10,000, kawo yanzu an samu mutuwar mutane 10,210 a kasar Afrika ta kudu.

Daga cikin jimillar adadin, an samu mutuwar mutane 301 cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji Mkhize.

Haka zalika, baki daya an samu adadin mutane 553,188 da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a kasar, ko a ranar Juma'a an samu adadin mutane 7,712 da suka kamu da cutar, a cewar ministan.

Lardin Gauteng, cibiyar tattalin arzikin kasar, shi ne wajen da annobar ta fi kamari inda yake da yawan mutane 190,999 da aka tabbatar sun kamu da cutar, sai yankin Western Cape dake bi masa baya da yawan masu dauke da cutar 99,588, yankin KwaZulu-Natal yana da jimillar mutane 95,648 wadanda aka tabbata sun harbu da annobar, yayin da yankin Gabashin Cape an samu yawan masu dauke da cutar 82,074.

Sai dai a halin yanzu jimillar mutanen da suka warke daga cutar ya kai 404,568, wato kashi 73 na yawan mutanen da suka harbu da cutar a kasar sun warke, in ji minista Mkhize.

Kawo yanzu, yawan mutanen da aka yiwa gwajin cutar a kasar sun kai 3,220,265, a ranar Juma'a kadai an yi sabbin gwajin cutar guda 36,607 a kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China