Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka harbu da COVID-19 a Afrika ya karu zuwa dubu 463
2020-07-06 13:10:15        cri
Ya zuwa ran 5 ga wata, bisa alkaluman da cibiyar kandagarkin cututuka ta Afrika ta bayar, kasashe 54 na nahiyar sun sanar da yawan mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 463306, daga cikinsu 11086 sun mutu, yayin da 222304 suka warke daga cutar.

Ya zuwa yanzu, cutar ta fi kamari a kudancin Afrika, sai kuma a arewacin Afrika. Kasashen da suka fi fama da wannan cuta su ne Afrika ta kudu, da Masar da Najeriya da Ghana da sauransu.

Hukumar tsara shirin abinci ta duniya ta MDD wato WFP ta ba da rahoto a kwanakin baya cewa, saboda barkewar wannan mumunar cuta, mutane miliyan 57.5 a tsakiya da yammacin Afrika za su yi fama da karancin hatsi, inda a gabashin Afrika wannan adadi zai kai miliyan 41.5. Ban da wannan kuma, bala'in ambaliyar ruwa da sauran bala'u daga indallahi da ma bala'in fari mafi tsanani da ba a taba ganin irinsa a cikin goman shekaru da suka gabata ba, za su kawo barazana wajen samar da isassun hatsi a nahiyar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China