Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan masu COVID-19 a Afrika ya doshi 970,000
2020-08-05 09:55:04        cri

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a fadin Afrika ya kai 968,020 ya zuwa ranar Talata.

Africa CDC, kwararriyar hukumar lafiya ta kungiyar AU mai mambobi kasashen Afrika 55, a bayaninta na baya bayan nan da ta fitar ranar Talata ta ce, adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a fadin nahiyar ya karu daga 957,035 a ranar Litinin zuwa 968,020 a ranar Talata.

Hukumar ta bada rahoton cewa yawan mutanen da cutar COVID-19 ta hallaka a Afrika ya kai 20,612 ya zuwa ranar Talata, daga adadin 20,288 a ranar Litinin.

Cibiyar dakile cutukan ta nahiyar Afrika ta kara da cewa, majinyata 629,726 sun warke daga cutar ta COVID-19 a fadin nahiyar ya zuwa yanzu, bayan samun sabbin mutanen da suka warke kimanin 18,000 idan an kwatanta da yawan jimillar mutanen da suka warke 611,957 ya zuwa ranar Litinin.

Afrika ta kudu ce kasar da ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar, sai kasashen Masar, Najeriya, Algeria da Morocco dake bi mata baya. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China