Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Najeriya: Neman kudin diyya daga kasar Sin kan COVID-19 zai illata kokarin da duniya ke yi na yakar cuta
2020-07-21 13:31:02        cri
Jiya Litinin, darektan cibiyar nazarin kasar Sin ta Najeriya Charles Onunaiju, ya wallafa wani bayani a jaridar "Peoples Daily", mai taken "COVID-19: Neman kudin diyya daga kasar Sin kan cutar zai illata kokarin da duniya ke yi na yakar ta".

Bayanin ya nuna cewa, hadaddiyar kungiyar masanan shari'a da doka ta Najeriya, ta kai kasar Sin kara a gaban kotu, tana mai fatar Sin din ta biya kudin diyya har dala biliyan 200 ga Najeriya game da yaduwar cutar COVID-19. A ganin Charles Onunaiju, matakin kungiyar kuskure ne maras tushen doka, kuma zai illata kokarin da duniya ke yi wajen yakar cutar.

Onunaiju ya kara da cewa, Sin ta sanarwa WHO halin da take ciki game da yakar cutar ba tare da bata lokaci ba, kuma a fili bisa ka'idar adalci da daidaito, da sauke nauyin dake wuyanta. Ta kuma sanarwa sauran kasashen duniya jerin lambobin kwayar halittar cutar, da kuma katse hanyar yaduwarta cikin kankanin lokaci.

A daya bangaren kuma, Sin ta yi babbar asara sanadiyyar yaduwar cutar a cikin gidanta, ko da yake hakan ya haifar da babbar gudunmawa wajen aiwatar da dabarun hana saurin yaduwar cutar a duniya.

Bayanin ya kuma bayyana cewa, abun da kungiyar ta yi ya lahanta hadin kai da kasashen duniya ke yi wajen yakar cutar, kuma mataki ne maras tushe bisa doka, kuma babu hangen nesa a cikinsa. A ganinsa, wannan mataki ba zai samu nasara ba, kuma dora laifi kan kasar Sin, mataki ne na rashin wayewar kai. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China